logo

HAUSA

Babban bankin Najeriya ya baiwa ma`aikatar aikin gona na kasar takin zamani na kusan naira biliyan 100

2024-03-14 09:57:00 CMG Hausa

Babban bankin tarayyar Najeriya ya sanar da bayar da buhunan takin zamani miliyan 2.15 da aka kiyasta kudin su kan sama da naira buliyan 100 ga ma`aikatar harkokin noma da samar da abinci na kasar.

Gwamnan bankin Mr Olayemi Cardoso ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba 13 ga wata lokacin da ya kai ziyara ma`aikatar gonar ta tarayya, ya ce bankin ya dauki wannan mataki ne domin bunkasa harkokin noma tare da rage hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Gwamnan babban bankin na tarayyar Najeriya ya ce bankin yana bin dukkan matakan da suka zama wajibi domin tabbatar da daidaiton farashin a kasuwannin kasar, kasancewar rashin tabbas na farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi yana taka rawa sosai wajen faduwar darajar kudin kasar da kuma tsadar kayayyaki.

Ya ce babban burin kowanne magidanci shi ne ya fi karfin abin da zai ci ya kuma sha a dan kankanen farashi, inda ya tabbatar da kudirin babban bankin na hada kai da ma`aikatu da hukumomin gwamnati domin kyautata sha`anin noma domin wadatar kasa da abinci.

Da yake jawabi, ministan harkokin noma da samar da abinci Sanata Abubakar kyari ya yaba mutuka bisa wannan taki da babban bankin ya bayar domin rabawa ga manona na hakika.

“ Ina tabbatar maka da cewa za a rabar da kayan bisa adalci ga ainihin wadanda ake bukatar su amfana ta yadda za su samu cin gajiyar wannan babban tagomashi”

Ministan ya shaidawa gwamnan babban bankin cewa a halin yanzu akwai wani shiri mai taken shirin bunkasa noma na kasa wanda yake samun tallafin bankin raya kasashen Afrika, wanda karkashin shirin manoma na samun rangwamen kaso 50 na dukkan kayayyakin aikin gona da aka ba su.(Garba Abdullahi Bagwai)