logo

HAUSA

Ana amfani da na’urar hakar mai ta zamani da kamfanin Sin ya kera a Uganda

2024-03-14 16:03:27 CMG Hausa

Kwanan nan, an yi nasarar amfani da sabuwar na’urar “Xuanji” da kamfanin hakar mai na teku na kasar Sin ko CNOOC a takaice ya yi nazari da kuma kera da kansa a wurin hakar mai na Kingfisher na Uganda. 

Babbar jaridar yankin, wato jaridar “New Horizons” ta ba da rahoto a kwanan baya cewa, ingancin na’urar hakar man yana da muhimmanci sosai, a fannin inganci da tsaron aikin hakar mai na Uganda. An rage amfani da wutar lantarki da kashi 40 cikin dari idan aka kwatanta da ta tsohuwa, kuma karfin hako mai mafi girma ya karu da kashi 70 cikin dari. (Safiyah Ma)