logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoto Mai Taken “’Yancin Fadin Albarkacin Baki A Amurka: Gaskiya Da Hujjoji”

2024-03-14 21:12:51 CMG Hausa

A yau Alhamis, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wani rahoto mai taken “ ‘Yancin Fadin Albarkacin Baki a Amurka: Gaskiya da Hujjoji”. Rahoton wanda ya zayyana dimbin hujjoji, na da nufin bankado abun da “magana cikin ‘yanci” ke nufi ga Amurka, da ainihin abun da Amurka ke yi da kuma makasudin yin hakan.

A cewar rahoton, Amurka ta dade tana yayata ra’ayinta na ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma nuna fuska biyu, da lullube makarkashiyar siyasa da rashin adalci tsakanin al’umma ta hanyar wasu kalamai na siyasa marasa ma’ana da munafurci ta hanyar fakewa da “‘yancin fadin albarkacin baki”.

A cewar rahoton, a cikin Amurka, takkadamar siyasa na keta ‘yancin fadin albarkacin baki, tsoma baki da kafafen yada labarai ke yi cikin batutuwa na barazana ga fadin albarkacin baki, haka ma kafafen sada zumunta suna keta ‘yancin fadin albarkacin baki.

A tsakanin kasa da kasa kuma, har yanzu Amurka tana yaudarar kanta da wai tana magana da murya daya a madadin kowa, tana mai kawo tsaiko ga dangantakar kasa da kasa ta hanyar dabi’unta na babakere da lalata muhalin sauraron ra’ayoyin jama’ar duniya ta hanyar bata suna da yaudarar al’ummomin kasa da kasa ta hanyar daukaka kanta da zakin baki. (Fa’iza Mustapha)