logo

HAUSA

Kayayyakin wasanni kirar kasar Sin sun samu yabo a gasar wasannin Afirka ta 13

2024-03-14 14:39:44 CMG Hausa

Kayayyakin wasanni kirar kasar Sin da ake amfani da su yayin gasar wasannin Afirka ta 13 dake gudana yanzu haka a kasar Ghana, sun samu matukar yabo daga ‘yan wasa, da ma hukumomin gasar sakamakon ingancin su.

Yayin gasar wadda za a kammala a ranar 23 ga watan nan na Maris, ana iya ganin kayayyakin wasa nau’o’in daban daban, kama daga teburan wasan kwallon tebur har zuwa dandamalin wasan daga nauyi.

Da yake tsokaci kan hakan, mista Zhang Wei, babban manajan kamfanin “Taishan Sports Group”, kamfanin da aka baiwa aikin samar da kayayyakin wasan da ake amfani da su a gasar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua matukar farin cikin sa, bisa yadda aka zabi kamfanin sa ya gudanar da wannan aiki.

Zhang ya ce wannan ne karon farko da kamfanin Taishan ya gabatar da kayayyakinsa ga irin wannan gasa, kayayyakin da suka shafi sassan wasanni 23.

Da yake tsokaci game da hakan, ministan matasa da wasanni na kasar Ghana Mustapha Ussif, ya jinjinawa ingancin kayayyakin wasannin kirar kasar Sin, yayin taron manema labarai da ya gudana a ranar Litinin, yana mai cewa, kayayyakin sun zamo kadarorin wannan gasa ta nahiyar Afirka. Gasar wasannin nahiyar Afirka karo na 13, ta hallara sama da ‘yan wasa 4,000 wadanda ke fafatawa a nau’o’in wasanni 29. (Saminu Alhassan)