logo

HAUSA

Najeriya ta sanar da bude kan iyakokinta ta sama da na kasa da jamhuriyyar Nijar

2024-03-14 11:17:13 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin dage takunkumin da aka kakabawa jamhuriyar Nijar biyo bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne ranar Laraba 13 ga wata sakamakon shawarwarin da shugabannin kungiyar Ecowas suka zartar yayin taronsu a ranar 24 ga watan Faburairun 2024, umarnin kuma ya shafi kasashen Mali da Guinea.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Dage takunkumin yana kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban na tarayyar Najeriya Mr Ajuri Ngelale wanda kuma aka rabawa manema labarai a birnin Abuja, kuma umarnin ya fara aiki ne nan take.

A sakamakon hakan yanzu an budewa jamhuriyyar ta Niger dukkannin asusunta dake babban bankin Ecowas, sannan kuma an janye haramcin shiga ta fita ta kasa da ta sama zuwa kasar ta Nijar.

Sauran sun hada da dawo da cigaba da hada-hadar kasuwanci da ta kudade a hukumance tsakanin Najeriya da jamhuriyyar ta Nijar, kana da cigaba da baiwa kasar ta Nijar wutar lantarki daga Najeriya.

Haka kuma an baiwa jamhuriyar ta Niger damar amfani da kaddarorinta dake kasashen ketare wanda a baya aka haramta mata, sannan kuma yanzu kasar ta Nijar tana da damar samun tallafin kudade daga hukumomin kasa da kasa.

Haka zalika sanarwar ta dage takunkumin tafiye tafiye da aka kakabawa jami`an gwamantin kasar da iyalan su.

 Daga karshen shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da dage takunkumin hada-hadar kudade da sauran harkokin tattalin arziki da aka sanyawa kasar Guinea.(Garba Abdullahi Bagwai)