logo

HAUSA

Kasar Sin Na Kira Ga Amurka Ta Daina Danne Kamfanonin Waje Ba Bisa Adalci Ba

2024-03-14 19:31:59 CMG Hausa

Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayyana a yau Alhamis cewa, ya kamata Amurka ta girmama ka’idojin kasuwa da takara cikin adalci, ta daina durkusar da kamfanonin kasashen waje.

Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana hakan, inda ya ce, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba na kare halaltattun hakkoki da muradunta. (Fa’iza Mustapha)