logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada muhimmancin zurfafa hade fannin kere-keren kimiyya da fasaha da kere-keren masana’antu

2024-03-14 10:17:51 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira da a dora muhimmanci ga zurfafa hade fannonin kere-keren kimiyya da fasaha da na kere-keren masana’antu, a kuma gaggauta samar da sabon karfi, da sabbin alfanun ci gaba mai inganci.

Li, wanda kuma zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, ya yi tsokacin ne yayin da yake ran gadi a birnin Beijing a jiya Laraba.

Yayin ran gadin nasa, ya ziyarci cibiyar gudanarwa ta yankin gwajin sarrafa na’urorin tukin motoci da na’urori masu kwakwalwa, inda a cibiyar ya bukaci a karfafa kafa tsarin gudanarwa mai inganci, da tabbatar da karko, ta yadda za a kai ga bunkasa ci gaban masana’antun motoci, da gina birane masu gudana bisa na’urori masu kwakwalwa, karkashin tasirin daga martabar fasahohin sarrafa injuna da na’urori masu kwakwalwa.  (Saminu Alhassan)