logo

HAUSA

Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba

2024-03-13 21:13:24 CMG Hausa

Kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na Majalisar gudanarwar kasar Sin ya bayyana a yau Laraba cewa, kokarin da aka dade ana yi na karfafa kasar Sin da tabbatar da farfadowar al’ummar Sinawa da dunkulewar kasar ta Sin, abu ne da ba za a iya dakatar da shi ba.

Kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalsiar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau, inda ya ce duk da yanayin da ake ciki a mashigin tekun Taiwan, tubalin dangantakar da ke tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan da alkiblar raya ta ba su sauya ba, kuma ba za su sauya ba.

Ya ce babban yankin kasar Sin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da masu neman ‘yancin kan Taiwan da dakile masu tsoma baki daga waje, tare da bayar da goyon baya ga masu kishin kasa dake goyon bayan dinkewar Taiwan da babban yankin kasar da hada kan masu kishin kasa na Taiwan wajen inganta kyautata dangantakar yankin da babban yankin kasar Sin.

Chen Binhua, ya kuma bukaci mutanen Taiwan su fahimci abun da ya dace da su da wanda bai dace ba, su daukaka muradun al’ummar Sinawa da hada hannu da mutanen babban yankin kasar wajen tabbatar da dunkulewa da farfadowar kasa. (Fa’iza Mustapha)