logo

HAUSA

Shugaban Angola Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

2024-03-12 19:35:01 CMG Hausa

Shugaban jamhuriyar Angola, Joao Lourenco zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 14 zuwa 17 ga watan nan na Maris, bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Yayin taron manema labarai na yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya ce, a lokacin ziyarar, shugaba Xi zai shirya liyafar maraba ga shugaba Lourenco. Kana shugabannin biyu za su tattauna tare da halartar bikin murnar rattaba hannu kan daftarorin hadin gwiwa.

A cewar Wang Wenbin, kasashen biyu sun cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyya a bara, don haka Sin na sa ran ziyarar za ta kara sabon kuzari ga dangantakar dake tsakaninsu ta kowacce fuska tare da ingiza sabon ci gaba a hadin gwiwar abota dake tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)