logo

HAUSA

An yi kira ga ‘yan kasuwar Zimbabwe da su rungumi hadin gwiwa da sassan kasa da kasa bayan dage takunkuman Amurka

2024-03-12 11:08:50 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar harkokin waje da cinikayyar kasa da kasa na Zimbabwe Frederick Shava, ya yi kira ga sassan ‘yan kasuwar kasar sa da su rungumi hadin gwiwa da sauran takwarori na sassan kasa da kasa, don cin gajiya daga damammakin hadin gwiwa, bayan da Amurka ta dagewa Zimbabwe wasu manyan takunkumai da kasar ta sha fama da su tun daga shekarar 2003.

Mista Shava ya yi wannan kira ne a jiya Litinin, yayin bude dandalin ‘yan kasuwar Zimbabwe da na Amurka, wanda ya gudana a birnin Harare fadar mulkin kasar.

A yanzu haka dai wata kungiya mai zaman kanta ta ‘yan kasuwa mai lakabin ABC daga birnin Atlanta na Amurka, na gudanar da ziyarar lalubo damammakin zuba jari a Zimbabwe, kuma wannan ce tawagar ‘yan kasuwa ta farko da Zimbabwe ta karbi bakunci, tun bayan da gwamnatin Amurka ta dagewa kasar takunkumai a makon da ya gabata, kuma baya ga Zimbabwe, gungun ‘yan kasuwar su 9 za su isa kasashen Afirka ta kudu da Zambia.

To sai dai kuma duk da cewa gwamnatin shugaba Joe Biden na Amurka ta ayyana dage takunkuman ga Zimbabwe a ranar 4 ga watan nan na Maris, a daya hannun ta kakaba sabbin takunkumai kan ‘yan kasar 11, ciki har da shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa, da mataimakin sa Constantino Chiwenga, da wasu kamfanonin kasar 3, bisa zargin aikata laifukan cin hanci da keta hakkokin bil adama.  (Saminu Alhassan)