logo

HAUSA

Annobar sankarau ta hallaka mutane 22 a Yoben Najeriya

2024-03-12 09:57:00 CMG Hausa

Rahotanni daga jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, na cewa daga watan Disamban shekarar 2023 zuwa yanzu, annobar ciwon sankarau ta hallaka a kalla mutane 22 a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya Litinin a Damaturu fadar mulkin jihar ta Yobe, jimi’in lura da barkewar cututtuka da gabatar da gargadi a jihar Haruna Umar, ya ce an tabbatar da harbuwa mutane 636 da cutar a sassan kananan hukumomin jihar 6, tun bayan barkewarta a wannan karon.

Umar ya kara da cewa, cikin wadanda suka kamu da cutar, a kalla mutane 564 sun warke bayan jiyya, akwai kuma wani adadi na wadanda ake lura da su, ake kuma yi musu jinya a kebantattun cibiyoyi dake jihar. (Saminu Alhassan)