logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya bukaci gwamnonin kasar da su kawo karshen matsalolin rikicin manoma da makiyaya

2024-03-12 09:14:17 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohin kasar musamman wadanda suke fama da matsalolin hare-haren ’yan bingida da rikicin manoma da makiyaya da su yi kokarin kawo karshen wadannan matsaloli.

Shugaban ya bukaci hakan ne ranar Litinin 11 ga wata a garin Minna, fadar jihar Niger dake arewa ta tsakiyar Najeriya yayin kaddamar da kayayyakin aikin gona da kuma sabon filin jirgin sama da gwamnatin jihar ta gina.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce, sai an yi maganin rashin fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya, gwamnati za ta iya cimma burinta na yakar yunwa gaba daya a kasar.

Ya ce irin wannan rikici na makiyaya da manoma abun takaici ya fi karfi a arewacin kasar, inda kuma a wannan yanki ne gwamnati ta fi dogara wajen noman abinci domin amfani a cikin gida da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.

Shugaba Tinubu ya ci gaba da cewa, hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati tabbatar da tsaron lafiyar kowanne dan kasa, a don haka ya kalubalanci gwamnoni da su kara azama sosai wajen bullo da wasu managartan matakai da za su inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunansu.

“Ku sake tsara makiyayan, sannan ku samar da wani tsari na kiwon shanu, ku samar mana da fili, ni kuma a matsayi na na shugaban kasa zai yi bakin kokari cikin makonni biyu zuwa uku zan gabatar muku da ingantaccen shiri da zai warware wadannan matsaloli.”

A jawabinsa gwamnan jihar ta Niger Umar Bago ya shaidawa shugaban kasar cewa, an samar da wadannan kayayyakin aikin gona na zamani ne domin bunkasa noman abinci, kuma a shirye gwamnatin jihar take ta hada kai da kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa wajen cimma wannan buri nata. (Garba Abdullahi Bagwai)