logo

HAUSA

Kasa da kasa na begen ci gaban kasar Sin mai inganci za ta kara kawo dama ga duniya

2024-03-12 19:46:52 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ta manyan taruka biyu na kasar Sin da aka gudanar a bana, kasa da kasa sun ga kasar Sin mai samun ci gaba da yin kirkire-kirkire da bude kofa da hadin kai, kuma suna sa ran ganin kyakkyawar makoma ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin, haka kuma suna begen bunkasuwar kasar Sin mai inganci za ta kara kawo dama ga duniya.

Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, rahoton aikin gwamnatin kasar Sin ya gabatar da burin ci gaban GDP na kimanin kashi 5 cikin dari, lamarin da ya shaida cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfi da kyakkyawar makoma.

Wang Wenbin ya kara da cewa, bisa rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, za a kara bude kofa ga kasashen waje da sa kaimi ga samun moriyar juna. Don haka, kasar Sin za ta bi ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na duniya, da fadada bude kofa da yin cinikin waje mai inganci, da kara jawo jarin waje, da sa kaimi ga raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, da kuma zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin bangarori daban daban da yankuna. (Zainab Zhang)