logo

HAUSA

Kasar Sin Na Karfafa Gwiwar Musaya Tsakanin Jama’arta Da Takwarorinsu Na Amurka

2024-03-11 19:48:43 CMG Hausa

Kasar Sin na fata tare da karfafa gwiwar ganin karin musaya tsakanin Sinawa da Amurkawa, tare da hada hannu wajen rubuta tarihin abota tsakanin al’ummomin kasashen biyu a sabon zamani da kuma tarihin hadin gwiwar moriyar juna tsakanin kasashen.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Litinin, a lokacin da yake tsokaci kan wata wasika da magajin garin San Francisco na Californiar Amurka, London Breed da wasu jama’a daga dukkan bangarori daban daban suka aikewa shugaban kasar Sin, Xi Jinping.

Cikin wasikar da suka aike a ‘yan kwanakin da suka gabata, sun bayyana cewa, jawabin da shugaba Xi ya gabatar a liyafar maraba da kungiyoyin abokai a Amurka suka shirya masa a watan Nuwamban bara, ya mayar da hankali kan gina tubalin dangantakar kasar Sin da Amurka, bisa mu’amalar jama’ar kasashen biyu. Sun ce, birnin San Francisco, zai iya samar da dandali na musammam na musaya tsakanin kasashen biyu, kuma a shirya yake ya karfafa abotar kasashen biyu ta hanyar musaya tsakanin jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)