logo

HAUSA

Gayyato Wasu Kasashe Daga Waje Domin Shiga Tsakani Kan Batun Tekun Kudancin Kasar Sin Zai Kara Ta’azzara Lamura

2024-03-11 20:06:01 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, batun tekun kudancin kasar Sin, batu ne da ya shafi Sin da wasu kasashen kudu maso gabashin Asiya ko ASEAN.

Kakakin ma’aikatar Wang Wenbin ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Litinin, lokacin da aka masa tambaya game da raya albarkatun mai da iskar gas dake tekun kudancin kasar Sin.

A cewarsa, kasar Sin na nacewa ga daidaita takkadamar da ta shafi harkokin teku, ciki har da raya albarkatu, da kasashen da batun ya shafa kai tsaye ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna. Ya ce bai kamata amfani da albarkatu cikin tekun ya keta cikakken iko da hakkoki da muradun kasar Sin ba, bare kuma a kai ga gayyatar wasu kasashe don shiga cikin batun.

Ya kara da cewa, gayyatar wasu kasashe daga wajen yankin don shiga tsakani game da batun zai kara ta’azzara lamura. (Fa’iza Mustapha)