logo

HAUSA

Gabon: An ayyana ranar tattaunawa game da batun kawo karshen wa’adin rikon kwarya

2024-03-11 11:14:00 CMG Hausa

Shugaban rikon kwarya a kasar Gabon Janar Brice Clotaire Oligui Nguema, ya sanya hannu kan dokar da ta ayyana ranaikun 2 zuwa 30 ga watan Afirilu mai zuwa, a matsayin lokacin da za a gudanar da tattauna ta daukacin sassan kasar, game da batun kammala wa’adin rikon kwarya, da gudanar da babban zabe.

A jiya Lahadi ne shugaban na Gabon ya rattaba hannu kan dokar, wadda makasudin ta baya ga tabbatar da wa’adin kammalar rikon kwarya, akwai kuma saita alkiblar siyasa da tattalin arziki, da tsarin cudanyar kungiyoyin al’ummar kasar bayan kammalar rikon kwarya.

Kafin hakan, an tsara gwamnatin rikon kwaryar kasar za ta yi aiki ne na tsawon watanni 24, wa’adin da zai kare a watan Agustan shekarar 2025 dake tafe, inda za a gudanar da sahihin zabe da daukacin ‘yan kasar za su amince da shi.  (Saminu Alhassan)