logo

HAUSA

Kasar Sin ta zuba sabon kuzari ga tattalin arzikin duniya

2024-03-11 12:42:05 CMG Hausa

Manyan taruka biyu na kasar Sin tagogi ne da duniya ta samu na fahimtar Sin, kuma dandaloli ne da Sin ta tattauna tare da duniya, wadanda suka jawo hankalin duk fadin duniya.

A shekarar bana, manema labarai fiye da 3000 daga kasar Sin da kasashen ketare, sun yi rajistar yin intabiyu a manyan taruka biyu na kasar Sin, a ciki kuma, yawan manema labarai na cikin gida ya kai fiye da 2000, kuma yawan manema labarai daga Hong Kong da Macao da yankin Taiwan, da kuma kasashen waje ya kai fiye da 1000.

A ranar 5 ga watan Maris, shafin intanet na jaridar “The Wall Street” ta Amurka ta ba da rahoto mai taken “Makasudin karuwar tattalin arkikin Sin ya kai kashi 5 cikin dari, wanda ya nuna kwarin gwiwar gwamnatin kasar”, inda aka bayyana cewa, jimillar ta yi sama da hasashen da asusun IMF da sauran hukumomin kasa da kasa suka yi a baya, wanda ya nuna kwarin gwiwar gwamnatin Sin wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Kaza lika yayin manyan taruka biyu na kasar Sin, wasu manyan kafofin watsa labarai na kasashen waje sun gudanar da rahotanni ta hanyar watsa bidiyo kai tsaye, da hira da manema labarai dake wurin taron ta yanar gizo da sauransu, inda aka ambaci tunanin “sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko”, kuma aka yi tsokaci da cewa, tunanin shi ne abu mai muhimmanci a fannin raya tattalin arzikin Sin mai inganci.

Bugu da kari, manyan tarukan biyu na kasar Sin na bana, sun dawo kan tsarin tattaunawa ido da ido, inda aka tsara ayyuka a jere, kamar shirya “intabiyu da wakilan jama’a na NPC”, da “intabiyu da mambobin CPPCC”, da “intabiyu da ministocin gwamnati”, da tarukan manema labarai, da bude zauren tawagogin wakilan NPC da na mambobin CPPCC da dai sauransu ga manema labaru, ta yadda manema labarai na kasar Sin da na waje za su tattauna da wakilai, da mambobi da ministoci fuska da fuska.

Dandalin manyan tarukun biyu na kasar Sin ya yada “muryoyin Sin” zuwa dukkanin fadin duniya ta kafofin watsa labarai na duniya, kuma ya nuna wa duniya wata kasar Sin mai gaskiya, da budewa, da kuma kwarin gwiwa. (Safiyah Ma)