logo

HAUSA

'Yan majalisar dokokin kasar Sin sun amince da rahoton aikin gwamnati

2024-03-11 16:07:07 CMG Hausa

A yau Litinin ne a wajen rufe taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, 'yan majalisar dokokin kasar Sin suka zartas da kuduri kan rahoton aikin gwamnati, kazalika, sun zartas da dokar da aka yi wa kwaskwarima ta majalisar gudanarwar kasar, ta kuma amince da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekarar 2024, da amincewa da babban kasafin kudin shekarar 2024, har ila yau, sun zartas da kuduri kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama 'ar kasar Sin (NPC), da zartas da kuduri kan rahoton ayyukan kotun kolin jama'ar kasar, da kuduri kan rahoton majalisar masu shigar da kararrakin jama’a na kasar. (Yahaya)