logo

HAUSA

AU ta bayyana matukar damuwa game da barazanar tsaro ga ci gaban Afirka

2024-03-11 09:50:51 CMG Hausa

Majalissar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar Afirka AU, ta bayyana matukar damuwa game da yadda matsalar tsaro ke yiwa ci gaban zamantakewa, da tattalin arzikin sassan nahiyar Afirka kafar ungulu.

Majalissar ta yi tsokacin ne cikin wata sanarwar bayan taro da ta fitar a ranar Asabar, bayan taron da ta gudanar a baya bayan nan, don gane da rikicin da ya dabaibaye gabashin janhuriyar dimokaradiyyar Congo.

Ta ce abun takaici ne ganin yadda tashe tashen hankula ke kara tsananta a sassa daban daban na Afirka, don haka ta jaddada matsayar kasashe mambobin AU su 55, ta yin aiki tukuru don ganin an cimma kudurorin dake kunshe cikin ajandar bunkasa nahiyar ta shekaru 50, wato nan zuwa shekarar 2063, wadda ta mayar da hankali matuka ga cimma burikan wanzar da zaman lafiya da tsaro, ciki har da kawo karshen jin amon bindigogi a sassan Afirka nan zuwa shekarar 2030. (Saminu Alhassan)