logo

HAUSA

Shugaban Sin Ya Taya Asif Ali Zardari Murnar Lashe Zaben Shugaban Pakistan

2024-03-10 15:28:04 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Asif Ali Zardari murnar lashe zaben shugaban kasar Pakistan.

Cikin sakon taya murnar a yau Lahadi, shugaba Xi Jinping, ya ce Sin da Pakistan, makwabtan juna ne na kwarai, kuma aminai. Haka zalika, abokan hulda ne kuma ‘yan uwan juna, yana mai cewa, abota mai karfi dake tsakanin kasashen biyu wani zabi ne da suka yi na tarihi, kana abu ne mai daraja ga al’ummominsu.

Shugaban na kasar Sin ya kuma yaba da ci gaban dangantaka da aka samu tsakanin Sin da Pakistan, inda ya ce a shirye yake ya hada hannu da shugaba Zardari wajen daukaka daddadiyar abotar dake tsakanin kasashensu, da inganta hadin gwiwarsu a bangarori da dama da ingiza hulda bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu cikin ko wane yanayi da kuma gaggauta gina al’ummar Sin da Pakistan mai makoma ta bai daya bisa adalci a sabon zamani, domin amfanawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)