logo

HAUSA

Jakadu daga kasashe 11 da EU sun ziyarci jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya

2024-03-10 15:44:11 CMG Hausa

Wata babbar tawagar jakadu daga kasashen waje 11 da kungiyar tarayyar Turai sun ziyarci Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya domin nazari a kan yanayin rayuwar ‘yan gudun hijira da kuma wadanda rikici ya yi sanadin kauracewa muhallansu.

Gwmanan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne ya karbi bakuncin tawagar dake karkashin jagorancin jakadan Burtaniya a Najeriya Richard Montgomery.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Jakadun da suka kunshi na kasashen Belgium da Canada da Faransa da Jamus da Ireland da kuma Masar.

Sauran su ne Japan da Norway da Sifaniya da Amurka da Burtaniya da kuma wakilan kungiyar tarayyar Turai. Sun isa garin na Maiduguri ne bisa gayyatar gwamna farfasa Babagana Umara Zulum da zummar tattaunawa a kan shirye-shiryen gwamnatin jihar na samar da kyakkyawar makoma mai dorewa ga al’umomin da hare-haren ta’addanci na ‘yan kungiyar Boko Haram ya daidaita sama da shekaru 13 da suka gabata.

A lokacin da ya jagoranci ayarin jakadun zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Muna wanda yake dauke da sama da ‘yan gudun hijira dubu 100 da suka kunshi mata da kananan yara, gwamnan na jihar Borno ya shaidawa jakadun cewar tallafin da ‘yan gudun hijira ke samu daga kungiyoyin bayar da agaji na duniya ya ragu mutuka, lamarin da ya haifar da yunwa a irin wadannan sansanoni.

A jawabinsa jakadan kasar Burtaniya a Najeriya Mr. Richard Montgomery ya ce kwamatinsu zai zauna ya sake bullo da wasu hanyoyin da za a taimakawa jihar ta Borno wajen ayyukan jin kai.

“Mun ji dadin kasancewarmu a wannan jiha, kuma mun yi tattauna sosai masu ma’ana a game da shirye-shiryen da gwamnan jihar ke kokarin bujiro da su domin samar da managartan matakai da za su kyautata rayuwar mutanen da tashe-tashen hankula ya shafa a tsawon sama da shekaru 10 da suka gabata.” (Garba Abdullahi Bagwai)