logo

HAUSA

An bude gasar wasannin Afirka karo na 13 a Ghana

2024-03-09 15:50:47 CMG Hausa

A daren Juma’a ne aka bude gasar wasannin Afirka karo na 13 a Accra, babban birnin kasar Ghana, inda taron ya hada dubban dubatar ‘yan wasa, da jami’ai, da masu sha’awar wasannin motsa jiki a fadin nahiyar domin murnar wannan gagarumin biki.

A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya ce gasar ta ba dama ga Afirka ta yi amfani da wasanni wajen hada kan nahiyar.

Gasar wasannin Afirka karo na 13 mai taken "Fuskantar Mafarkin Afirka" za ta samu halartar 'yan wasa sama da 4,000 da za su fafata a fannonin wasanni 29, takwas da suka yi nasara za su shiga gasar Olympics ta bazara ta Paris 2024. (Yahaya)