logo

HAUSA

Sin ta baiwa duk duniya sako mai yakini

2024-03-08 11:19:15 CGTN HAUSA

 

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya amsa tambayoyin da ’yan jarida na gida da waje suka yi masa, a gun taron manema labarai da aka gudanar kan manyan taruka biyu wato na NPC da CPPCC, wadanda suka shafi huldar kasa da kasa da abubuwa masu jan hankalin mutane da daidaita harkokin duniya da sauransu. Amsoshin da ministan ya bayar dangane da tambayoyin da aka yi masa, sun baiwa duk fadin duniya sako mai yakini cewa, Sin tana taka rawar gani a duniya bisa bunkasuwarta mai karko.

“Sin za ta nace ga matsayin kasancewar karfi mai karko wajen ciyar da zaman lafiya da ci gaban duniya gaba”, kafofin yada labarai na kasa da kasa sun mai da wannan magana matsayin da Sin take dauka ta fuskar diplomasiyya.

A halin yanzu, ana ci gaba da fama da rikicin Ukraine, baya ga rikicin Palasdinu da Isar’ila dake kara tsananta, kuma siyasar yankuna na kara kamari. Ba fatan tabbatar da tsaro da zaman lafiya cikin kasarta kadai Sin ke yi ba, har ma da son taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duk duniya

A gun taron manema labarai, Sin ta gabatar da wata hanya mai salon kasar wajen magance matsalolin dake jan hankalin mutane, wato nacewa ga hana tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, da warware rikici a siyasance bisa adalci da daidaito, ta yadda za a daidaita batutuwa daga tushe.

Manufar da Sin take dauka wajen magance harkokin duniya ita ce, gudanar da harkokin duniya tsakanin bangarori daban-daban cikin adalci bisa oda da doka, da samun ci gaban tattalin arzikin duniya tare bisa ka’idar hakuri da juna, matakin da ya dace da halin da ake ciki, kuma ya bayyana muradun kasashe masu tasowa baki daya.

Kazalika, duniya na fama da karancin karfin samun bunkasuwa, kana wasu kasashe na daukar matakin katse hulda, game da hakan, Sin ta bayyana matsayin da ta kan dauka cewa, dole ne a kafa tsarin tattalin arziki mai bude kofa.

Bugu da kari, a shekarar bara, yawan bunkasuwar Sin ya kai kashi 5.2%, wanda ya taka rawa na kashi 1/3 ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, hakan ya sa Sin take taka rawar gani wajen ingiza bunkasuwar duniya.

Yanzu, duniya na shiga wani yanayi mai cike da mabambantan sauye-sauye, jama’ar duniya na ganin muhimmancin kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, da fahimtar rawa mai dorewa da Sin take bayarwa. A lokacin bazarar bana, wadannan manyan taruka biyu na fitar da sako mai yakini ga duk fadin duniya cewa, Sin za ta ci gaba da ingiza bunkasuwar duniya mai dorewa ba tare da sauyawa ba. (Amina Xu)