logo

HAUSA

Layin dogo tsakanin Lagos da Ibadan na kasar Nijeriya ya yi aiki yadda ya kamata fiye da kwanaki 1000

2024-03-07 10:53:55 CMG Hausa

Bisa yunkurin aiwatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, an fara aiki da layin dogon dake tsakanin Lagos da Ibadan na kasar Nijeriya a watan Yunin shekarar 2021, wanda kamfanin CCECC na kasar Sin ya gina. Tsawon layin ya kai kilomita 157, wanda yake aiki bisa ma’aunin hanyoyin jiragen kasa na zamani, kuma saurin tafiyar jiragen kasa kan layin bisa shirin da aka tsara ya kai kilomita 150 a kowace awa. Ya zuwa ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2024, layin dogon ya yi aiki yadda ya kamata har na tsawon kwanaki 1000, kana yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga kan layin ya zarce miliyan 2, inda yawansu a wata-wata ya kai dubu 150, kana an sayar da tikitin fiye da kashi 80 cikin dari na jiragen kasa dake tafiya kan layin.

Ba kawai kawo sauki ga jama’a wajen yin zirga-zirga layin dogon ya yi ba, har ma da inganta jigilar kayayyaki tsakanin mashigin teku da yankunan kasar, tare da gaggauta raya masana’antu da tattalin arziki a Nijeriya. (Zainab Zhang)