logo

HAUSA

Majalissar wakilan Najeriya ta bukaci saka mambobinta cikin tsarin sayar da shinkafa da hukumar kwastam ke gudanarwa

2024-03-07 09:56:45 CMG Hausa

Majalissar wakilan tarayyar Najeriya ta bayyana damuwa bisa ci gaba da fuskantar karancin abinci duk kuwa da matakan da gwamnati take dauka na dakile kafofin da suke haifar da tsadar kayayyakin masarufi a kasar.

Mataimakin shugaban mjalissar Hon Benjamin Kalu ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa ta musamman da majalissar ta gudanar da ministan ayyukan gona na kasar da kuma shugaban hukumar Kwastam. Ya ce, ya zama wajibi a sake inganta taswirar shirin wadata kasa da abinci domin yin riga-kafin yunwa a tsakanin al’umma.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Mataimakin shugaban majalissar wakilan ta tarayyar Najeriya wanda ya yaba da shawarar da gwamnatin tarayyar ta yanke na baiwa hukumar kwastam damar sayar da kayan abincin da aka kama daka wajen masu fasa-kauri, inda ya ce, hakika wannan mataki ne da zai rage kaifin tsadar kayan abinci a cikin gida.

Sai dai kuma ya bukaci hukumar ta kwastam ta saka wakilan majalisar cikin shirin sayar da kayan abincin ga al’umomin da suke wakilta.

“Wakilan majalissar dokokin ta kasa za su kasance cikin tsarin sayar da kayan abinci ga al’umomin mazabunsu.”

Da yake jawabi a gaban ’yan majalissar, shugaban hukumar kwastam na tarayyar Najeriya Bashir Adewale Adeniyi ya ce, kwanan nan hukumar ta kama wasu manyan motocin dakon kaya guda 120 makare da kayan abinci ana kokarin fitar da su daga Najeriya zuwa kasashe makwafta.

“A game da kayayyakin cimaka da aka shigo da su kasar nan ta haramtacciyar hanya, kuma muka sami nasarar kamawa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba mu umarnin mu sayar da su kai tsaye ga ’yan Najeriya masu tsananin bukata.”

Shi kuwa ministan harkokin gona na tarayyar Najeriya Sanata Abubakar Kyari ya tabbatarwa ’yan majalissar cewa daga yanzu a Najeriya za a rinka gudanar da noman abinci a gaba dayan watanni 12 na shekara maimakon watanni 4, za kuma a cimma hakan ne kuwa ta hanyar amfani da dukkanin madatsun ruwan da a baya ba a amfani da su a kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)