logo

HAUSA

An yi bikin rantsar da sabbin mambobi guda 8 na hukumar COLDEFF

2024-03-07 19:20:01 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijer, wasu sabbin mambobin Coldeff sun yi shigowarsu a cikin hukumar a ranar Laraba 6 ga watan Maris din shekarar 2024, a yayin wani bikin rantsar da su da ya gudana a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai din abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, kuma shugaban kasa, birgadiye janar Abdourahamane Tiani, ya jagoranci wannan kebabben biki a zauren taro  na fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, na rantsar da sabbin mambobin hukumar da ke yaki da cin haci, da yaki da satar dukiyar kasa da kuma aka dora ma nauyin karbo dukiyar kasa ta COLDEFF su guda 8 mata biyu da maza shida.

‘Yan kasar Nijar da dama ne suke cike da fatan alhari da nuna goyon baya ga hukumar COLDEFF bisa ga wannan babban nauyi da hukumomin kasa suka dora mata.

Bikin ya gudana a gaban idon mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP, mambobin gwamnatin wucin gadi da shugaban kungiyar addinin musulunci ta kasa. (Mamane Ada)