logo

HAUSA

Nijar-Benin: Ferefen jihar Gaya na ziyarar gani da ido a birnin Malanville na kasar Benin

2024-03-06 09:17:51 CMG Hausa

Wata tawagar hukumomin jihar Gaya ta kasar Nijar mai iyaka da kasar Benin a karkashin jagorancin Kaftin Boureima Seyni ta isa birnin Malanville na kasar Benin a ranar jiya Talata 5 ga watan Maris din shekarar 2024. Bayan wata tawagar manyan jami’an kwastan na Nijar dake a yanzu a birnin Cotonou.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ferefen jihar Gaya a karkashin wata tawaga ya sauka birnin Malanville domin wani rangadin gani da ido, a cewar wasu majiyoyi.

Zango biyu ne suka shafi musamman ma wannan rangadi na ’yan sa’o’i kalilan na ferefen jihar Gaya mai iyaka da kasar Benin.

Nesa da idon manema labarai, ferefen Gaya, kaftin Boureima Seyni da kansa tare da mutanen dake rakiyarsa sun je tashar bincike dake bakin iyaka da kuma wurin ajiye manyan motoci na Bodjecali da ke Malanville da zumma tabbatarwa kansa a halin dake ciki a wadannan yankuna biyu dake makwabtaka da juna, tun bayan daidaituwar harkoki tsakanin kasar Nijar da kungiyar CEDEAO ko ECOWAS.

A cewar majiyoyi na kusa da hukumomin kasashen biyu, wannan ziyara ta ferefen jihar Gaya na kasancewa wata shimfidar share fage ga wasu tawagogin birnin Yamai nan da ’yan kwanaki masu zuwa.

Wannan tawaga ta samu tarbo daga hukumomi da manyan jami’ai na wurin.

Haka zalika, a cewar wasu rahotanni, ana shirin shirya wani taro a ranar Alhamis mai zuwa tsakanin hukumomin kasar Benin da na Nijar, domin tattauna yiyuwar maido da hada-hada tsakanin kasashen biyu.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.