logo

HAUSA

An bankado shirin Philippines game da tekun kudancin kasar Sin

2024-03-06 21:32:40 CMG Hausa

Jiya Talata 5 ga wata ne, kasar Philippines ta sake kutsa kai cikin yankin ruwan tekun dake kewaye da Ren’aijiao na tsibiran Nanshan na kasar Sin, a wani yunkuri na jigilar kayan gine-gine ga jirgin ruwan sojanta dake jibge a wajen ba bisa doka ba. Wannan yunkuri shi ne sabon matakin da kasar Philippines ta dauka a cikin shirinta kan tekun kudancin kasar Sin.

Ya zama dole Philippines ta gane cewa, Amurka kasa ce mai matukar son kai, wato manufofin da kasar ta tsara kan yankunan Asiya da tekun Pasifik, suna bautawa babakeren da Amurka take nunawa. Tarihi ya shaida cewa, duk wata kasa da Amurka ta taba amfani da ita, za kuma ta yi watsi da ita a karshe.

A halin yanzu, kasar Sin da kasashen ASEAN suna kokarin tsara “ka’idoji kan matakan da suka shafi tekun kudancin kasar Sin”. Ya kamata Philippines ta natsu, ta saurari muryoyin bangarori daban-daban, ciki har da kasashe makwabta. Firaministan kasar Malaysiya, Anwar bin Ibrahim ya bayyana a wajen taron koli na musamman na ASEAN da Australiya na wannan karo cewa, Malaysiya ‘yantacciyar kasa ce, wadda ba ta bin umarnin duk wata babbar kasa, kana, ba ta da matsala ko kadan da kasar Sin. (Murtala Zhang)