logo

HAUSA

Ana sa ran an yi tafiye-tafiye biliyan 8.4 yayin Bikin Bazara a kasar Sin

2024-03-06 11:06:43 CMG Hausa

Yayin da hada-hadar zirga-zirga ta lokacin bikin bazara ke zuwa karshe, ana sa ran an yi tafiye tafiye sama da biliyan 8.4 tsakanin yankunan kasar Sin a lokacin.

Alkaluman da ma'aikatar kula da sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Talata ne suka bayyana hakan.

Lokacin yawaitar zirga-zirgar ta shekara-shekara, wadda a bana da ta fara daga ranar 26 ga watan Janairu, ta kawo karshe ne a jiya Talata. A kan samu karuwar bukatar zirga-zirga ga mutanen dake komawa garuruwansu domin saduwa da iyalansu a lokacin.

Zuwa daren jiya Talata, an yi kiyasin an yi tafiye-tafiyen mota biliyan 7.83, da miliyan 480 da aka yi ta jiragen kasa, sai wasu miliyan 83 na jiragen saman fasinja, da kuma miliyan 29 da aka yi ta ruwa. (Fa'iza Mustapha)