logo

HAUSA

Kungiyar kwallon kafa ta kasa FENIFOOT ta yi allawadai da harin ’yan fashi da makami kan bas din dake dauke da ‘yan wasa AS SONICHAR

2024-03-06 10:06:51 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, kungiyar kwallon kafa ta kasa cewa da Fenifoot a yayin wani zaman taron gaggawa na ranar jiya 5 ga watan Maris din shekarar 2024 a cibiyarta dake birnin Yamai ta fitar da wata sanarwa domin bayyana damuwarta kan harin da aka kaiwa ’yan wasan AS SONICHAR na Tchirozerine.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto kan wannan sanarwa. 

Kwamitin zartarwa na kungiyar kwallon kafa ta kasa Fenifoot ya bayyana mamakinsa da bacin ransa game da harin da wasu ’yan fashi da makami sun kai kan motar dake dauke da tawagar ’yan wasan kwallon kafa na kungiyar SONICHAR ta jihar Tchirozerine, a ranar Asabar 2 ga watan Maris din shekarar 2024, bisa hanyarsu ta komawa gida bayan sun fafata wasa ta cin kofin kwallon kafar yankin Agadez.

A cewar wannan sanarwa, duk da ba’a samu asarar rayuka ba. Amma ’yan fashi da makami sun karbe saluloli da kudade da dama na ’yan wasa da masu horar da ’yan wasa, kafin su tsere bisa babura.

Kungiyar Fenifoot ta yi tir da allawadai da babbar murya kan wannan hari tare da kawo goyon bayanta ga tawagar ’yan wasan AS SONICHAR.

Haka kuma, kwamitin zartarwa na Fenifoot na fatan ganin an duba wannan matsala, da jami’an tsaro na jandarma na Tchirozerine suka fara bincike.

Tare da kawo goyon baya ga jami’an tsaro na FDS, bisa namijin kokarin da suke na yaki da ’yan fashi da makami.

A karshe dai sanarwar ta Fenifoot ta jinjinawa masu ruwa da tsaki da suka hada da ’yan wasa, masu horar da ’yan wasa, kocina, ’yan jaridan wasannin motsa jiki da sauransu da su ci gaba da kokarinsu duk da matsaloli da haduran da za su iyar fuskanta, domin kwallon kafa Nijar ta ci gaba.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar