logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kebbi ta yi alkawarin samun alaka mai kyau da ’yan kasuwar kasar China

2024-03-06 09:47:01 CMG Hausa

Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris ya tabbatarwa ’yan kasuwar kasar China samun yanayi mai kyau a duk lokacin da suke bukatar zuba jarinsu a jihar.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne a birnin Kebbi, fadar gwamnatin jihar lokacin da ya karbi bakuncin ayarin masu zuba jari daga hukumar bunkasa harkokin cinkayya tsakanin  China da kasashen Afrika, inda ya ce, gwamnatinsa a shirye take ta yi mu’amulla da wakilan hukumar domin kyautata sha’anin saka jari kai tsaye a jihar da ma kasa baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Dr. Nasir Idris ya ce, jihar ta Kebbi jiha ce mai dinbin arzikin noma tare kuma da tarin ma’adinan kasa da ake da su a daukacin kananan hukumomin jihar 21, inda ya tabbatar da cewa, da yawa daga cikin irin wadannan ma’adanai na kasa ba a iya cin moriyarsu saboda rashin masu saka jari a bangaren.

“Zuwanku jihar Kebbi babban ci gaba ne a gare ku, wannan gwamnati tamu daman dai tana  neman ’yan kasuwa irinku domin su zo  su zuba jarinsu a jihar.”

Gwamnan ya ce, za a zagaya da ’yan kasuwar na kasar China sassa daban daban na jihar domin dai su ganewa idanunsu irin arzikin da jihar ke da shi.

Da take jawabi jagorar ayarin ’yan kasuwar Mrs Li Zhensheng ta shaidawa gwamnan cewa sun kasance a jihar Kebbi ne tare da tsare-tsaren ayyuka masu ma’ana da za su taimaka wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar.

“Ha’ila yau kuma a shirye wannan hukuma take ta ci gaba da fadadawa tare da kyautata hadin kai tsakanin kasar China da kuma kasashen dake nahiyar Afrika.”

Ta ce irin wadannan hadin kai sun fi karfi ne a bangarorin aikin gona musamman noman rani, kyauta harkokin masana’antu da sauran fannonin ci gaban tattalin arziki. (Garba Abdullahi Bagwai)