logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina amfani da Phippines a matsayin dan amshin shata a tekun Kudancin kasar Sin

2024-03-06 21:19:05 CMG Hausa

A yau Laraba ne kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina amfani da Phillippines a matsayin dan amshin shata a batun tekun kudancin kasar Sin.

Mai Magana da yawun ma’aikata harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labarai cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da kada ta yi amfani da Philippines a matsayin dan amshin shata wajen tada rikici a tekun kudancin kasar Sin. Bai kamata Philippines ta bar kanta a hannu Amurka ta rika jujjuyawa ba.

Mao Ning ta ce, Ren'ai Jiao dai batu ne na tsakanin kasashen Sin da Philippines, ya kamata duk wani bangare na uku ciki har da Amurka, ya guji tayar da rikici, ko tsoma baki. (Yahaya)