logo

HAUSA

An yi kira ga kasashen Afirka da su lalubo tsare-tsaren samar da kudade domin ayyukan dakile sauyin yanayi

2024-03-05 10:29:05 CMG Hausa

Kwararru daga sassan nahiyar Afirka, sun yi kira ga kasashen nahiyar da su lalubo managartan tsare-tsaren samar da kudaden gudanar da ayyukan dakile mummunan tasirin sauyin yanayi.

Kwararrun sun yi kiran ne yayin taron da aka shirya, don tattauna hanyoyi masu dorewa na samar da kudaden kare muhalli daga gurbata, karkashin hukumar bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirka ta MDD ko UNECA a takaice.

Yayin taron, wanda ya gudana a birnin Victoria Falls na Zimbabwe a karshen makon jiya, daya daga masanan da suka halarta, kuma kwararren masani a hukumar ta UNECA Linus Mofor, ya shaidawa taron cewa, kasashen Afirka na fuskantar tasirin karuwar kamfar ruwa da tsanantar zafi a matakai daban daban, ciki har da fari da rashin tabbas na lokutan yanayi.

Mofor ya kara da cewa, adadin tallafi da kasashen Afirka ke samu daga sassan kasa da kasa, ba zai wadatar da bukatar nahiyar game da shawo kan kalubalen da muhallin halittu ke fuskanta ba. Haka zalika, irin wannan tallafi ba zai isa a shawo kan asara ko lalacewar yanayi ba. Bugu da kari, tallafin ba zai isa a tallafi bukatun rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayi a sassan kasashe masu tasowa ba.

Masanin ya ce samar da kudade, domin aiwatar da tsare-tsaren dakile mummunan tasirin sauyin yanayi, muhimmin mataki ne na wanzar da ci gaba. Har ila yau, hakan zai ingiza bukatar fitar da mafi karancin iskar carbon, da karfafa juriyar yanayi a sassan Afirka ta hanyar hada karfi da karfe tsakanin masu ruwa da tsaki na nahiyar.  (Saminu Alhassan)