logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya na kokarin tabbatar da karfafuwa tattalin arzikin kasar

2024-03-05 09:45:02 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya ce, garambawul din da gwamnatin kasar ke yi a cikin tsare-tsare da manufofinta zai taimaka matuka wajen karfafa tattalin arziki ta yadda dukkan ’yan kasa za su amfana.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin 4 ga wata a Gombe dake arewa maso gabashin kasar yayin kaddamar da shirin bayar da horo a kan sana’o’i daban daban ta amfani da kafar intanet tare kuma tallata fasaha da sana’o’in ’yan Najeriya a kasuwanin duniya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Sanata Kashim Shettima ya ce, sabbin sauye sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ta bullo da su, za su taimaka wajen samar da daidaito a fagen kasuwanci tsakanin Najeriya da sauran kasashen duniya.

Ko da yake dai mataimakin shugaban kasar ya ce, irin matakan da ake dauka na sake fasalta tattalin arzikin kasar suna da tsauri sosai, amma dai idan aka jure za su kai ga tattalin arzikin kasar ga tudun mun tsira, inda ya ce, kalubalen da ’yan kasa ke fuskanta a yanzu na dan takaitaccen lokaci ne.

A kan batun cibiyar kyautata sana’a da cinikayya ta kafar intanet kuwa wato Outsourcing Initiative, mataimakin shugaban kasar ya ce, shirin alama ce dake nuna mahimmin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

“Wannan manufa ce da za ta samar da miliyoyin guraben aikin yi da kuma bunkasa harkokin kasuwancin ’yan Najeriya da sauran sassan ayyuka da ake aiwatar da su ta amfani da fasahar zamani, lamarin da zai kai ga daukakar kasar zuwa matsayin da ba a taba zata ba.”

A jawabinsa gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya ce, shirin zai yi sanadin samar da kafofin aikin yi har dubu 2 ga matasa maza da mata a jihar ta Gombe, inda ya bayyana farin cikinsa bisa samar da cibyar a jihar irinta ta farko kuma mafi girma a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya. (Garba Abdullahi Bagwai)