logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta gano hanyar warware matsalolin wutar lantarki a kasar

2024-03-04 09:36:33 CMG Hausa

Ministan harkokin wutar lantarki na tarayyar Najeriya Mr Adebayo Adelabu ya ce, gwamnati ta yi odar tasoshin samar da wuta na tafi da gidanka har guda 10, a wani mataki na shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta a bangaren hasken wutar lantarki.

Ministan ya tabbatar da hakan ne a birnin Abuja yayin wani taro da ya gudanar da kwamashinonin lura da makamashi da wutar lantarki na wasu jihohi 23 dake  kasar, inda ya ce, domin cimma burin da aka sanya a gaba yanzu za a rinka aikin hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya wajen wadata kasa da wutar lantarki.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan wutar lantarkin na tarayyar Njeriya ya bukaci al’ummar kasar da su kara hakuri ana daf da warware dukkannin matsalolin da suke haifar da cikas wajen samar da wadatacciyar wuta a kowanne bangare.

Mr. Adebayo Adelabu ya ci gaba da bayanin cewa, gwamnati ta gudanar da zuzzurfan bincike domin gano matsalolin, wanda yanzu kuma ana kan matakin gyara ne, inda ya ce a baya an yi amfani da matakan wucin gadi ne wajen warware matsalar wutar ba tare da an bi diddigin al’amarin ba tun daga tushe.

Ya ce har yanzu ba a samar da karin layin dakon wuta ba wanda zai iya tallafawa wadanda ake amfani da su da jimawa.

“Amma yanzu muna kan gabar tattaunawa da wasu kamfanonin kasar China guda biyu domin aikin manyan tasoshin wuta na zamani a gabashi da yammacin kasar wadanda da zarar tasoshin da muke amfani da su sun samu matsala nan da nan sai a sauya zuwa sabbin da aka samar, amma fa wannan aikin ba aiki ne da za a kammala shi cikin watanni shida ba ko shekara guda, kuma aiki ne da yake bukatar makudan kudade, domin a yanzuhaka  idan har za a samar da tashar wuta mai karfin KV 330 ana bukatar a kalla tsakanin dala miliyan 30 ne zuwa miliyan 50.”

Ministan daga bisani ya bukaci jihohin kasar da su yi amfani da damarmakin da gwamnatin tarayyar ta samar musu wajen assasa tashohin samar da wuta mallakin kansu, inda ya bada misali da jihar Abia wadda yanzu haka take da tasha mai karfin Megawatt 188 wadda take samar da wuta tsawon sa’o’i 24 a kananan hukumomi 7 zuwa 8. (Garba Abdullahi Bagwai)