logo

HAUSA

Birnin Beijing na shirin samar da karin masana’antu da wuraren kere-kere masu amfani da fasahohin zamani 100

2024-03-04 14:21:55 CMG Hausa

Hukumar raya tattalin arziki da fasahohin sadarwa ta birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ta ce an tsara samar da karin masana’antu, da wuraren kere-kere masu amfani da fasahohin zamani na dijital har 100 a birnin tsakanin shekarar nan ta 2024 zuwa 2026.

Hukumar ta ce cikin shekarun 3 masu zuwa, za a bunkasa manufar kafa masana’antu da wuraren kere-kere na dijital, kazalika za a daga matsayin kamfanonin birnin zuwa mizanin dijital.

Yanzu haka dai birnin Beijing na kara karkata ga sarrafa hajoji, da amfani da na’urori masu aiki da fasahar kwaikwayon tunanin dan adam, inda a watan da ya gabata ma, kamfanin Xiaomi mai kera wayoyin salula, ya bude sabuwar masana’antarsa a birnin, wadda ke da na’urorin kera wayoyi irin na zamani, da ka iya samar da wayoyin salula kimanin miliyan 10 a duk shekara.

Hukumar ta ce, tun daga shekarar 2021 zuwa yanzu, an gina masana’antu, da wuraren kere-kere masu aiki da fasahohin dijital har 103 a birnin na Beijing.

A cewar ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwa ta Sin, kasar ce ke kan gaba a yawan adadin masana’antun dake amfani da na’urori masu kwaikwayon tunanin bil adama a duniya, inda take da irin wadannan masana’antu da wuraren kere-kere sama da 10,000. (Saminu Alhassan)