logo

HAUSA

An yi bikin tunawa da ranar mata ta kasa da kasa a Beijing

2024-03-03 16:41:37 CMG Hausa

Kungiyar hadin-gwiwar matan kasar Sin (ACWF) ta gudanar da babban taron tunawa da ranar mata ta duniya wadda za ta fado a ranar 8 ga watan Maris, gami da karrama wasu fitattun matan da suka bada babbar gudummawa a bangarori daban-daban a Beijing, inda membar majalisar gudanarwa, kana shugabar ACWF, Shen Yiqin, ta gabatar da muhimmin jawabi.

A jawabin nata, jami’ar ta taya daukacin matan kasar Sin barka da ranarsu, da taya rukunoni da daidaikun mutane wadanda suka samu lambobin yabo babbar murna, inda ta ce, shugaban kasar Xi Jinping ya kan mai da hankali sosai kan harkokin da suka shafi mata, da lura da su sosai, da taimakawa ci gaban ayyukan mata, ta yadda za su bunkasa daga dukkan fannoni.

Jami’ar ta kuma bayyana fatanta dake cewa, matan kasar Sin za su shiga cikin muhimman ayyukan zamanantar da kasarsu, da bada gudummawa ga samar da ci gaba mai inganci, da taka muhimmiyar rawa a harkokin iyali, da cimma burikansu ta hanyar aiki tukuru, ta yadda za su iya bada gudummawar hikima da karfinsu ga harkokin raya kasa da sake farfado da al’ummun kasar baki daya. (Murtala Zhang)