logo

HAUSA

Shugaban kasar Saliyo na fatan hadin gwiwar aikin gona da lardin Hubei na kasar Sin

2024-03-03 21:15:06 CMG Hausa

Shugaban kasar Saliyo Julius Mada Bio, ya bayyana fatan yin hadin gwiwa a fannin noma tsakanin kasarsa da lardin Hubei na kasar Sin a jiya Asabar bayan da ya ziyarci cibiyar kula da amfanin gona ta kwalejin kimiyyar aikin gona ta Hubei, inda ya samu labarin nasarori da aka samu a fannin noman shinkafa.

Bio, wanda ya kai ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 27 ga watan Fabrairu zuwa 2 ga Maris, ya samu lambar yabo ta digirin digirgir a ranar Asabar din daga jami’ar kimiyyar binciken kasa ta kasar Sin (Wuhan).

Da yaka jawabi a jami’ar, Bio ya ce ziyarar tasa a kasar Sin na da nufin karfafa huldar diflomasiyya da huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasahen biyu, tare da sa kaimi ga zurfafa mu’amala tsakanin jami’o’in kasashen biyu.

Ya kuma bayyana cewa tun lokacin da Saliyo ta shiga shirin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” a shekarar 2018, kasar ta “ci gajiya sosai daga ayyukan da ke karkashin wannan shiri.

Hubei da Saliyo suna abokantaka na dogon lokaci. A cikin shekaru masu yawa, lardin ya aika da kwararrun masana aikin gona zuwa Saliyo don ba da gudmmawar kwarewa a fannin noma da dabarun kiwo. Haka kuma, jami'ar kimiyyar binciken kasa ta kasar Sin (Wuhan) ta ba da horo ga kwararru sama da 20 daga Saliyo a fannonin da suka hada da albarkatun kasa da aikin injiniya da kimiyyar muhalli da injiniyanci da sauransu. (Yahaya)