logo

HAUSA

Masana sun yaba da rawar da kasar Sin ke takawa wajen samar da ababen hawa mara gurbata muhalli a UNEA-6

2024-03-03 17:24:31 CMG Hausa

An kara saurin sauya sheka zuwa amfani da abeben zirga-zirga masu amfani da makamashi mai tsafta, wanda ke inganta yanayin muhalli da lafiyar bil Adama a cikin birane, sabo da karuwar samar da motoci masu amfani da sabbin makamashi da kasar Sin ke kerawa, a cewa kwararru a taro na shida na majalisar kula da muhalli ta MDD wato UNEA-6 a babban birnin Kenya na Nairobi.

Kasar Sin ta taka rawar gani sosai wajen taimakawa kasashe masu tasowa, wadanda suka fi yawa a nahiyar Afirka, su rungumi ababen hawa masu amfani da wutar lantarki a birane, da rage fitar iskar carbon, a cewar Ali Mohamed, wakilin musamman kan harkokin yanayi na kasar Kenya dake ofishin shugaban kasar, a ranar Alhamis a taron UNEA-6.

Mohamed ya kara da cewa, kasar Sin ita ce tushen kusan dukkan motocin da ke amfani da wutar lantarki da ke zirga-zirga a titunan kasar Kenya, wanda ke taimaka wa yunkurin neman sauyi zuwa tsarin sufuri mara gurbata muhalli tare da kara ingancin iska. Ya ce, Kenya ta samar da wata manufa ta tallafi da tsarin ka'idoji don zaburar da ci gaban zirga-zirgar ababen hawa masu amfani da wutar lantarki baya ga saka hannun jari a masana'antar hada sassan motoci masu amfani da makamashin lantarki wato NEV na cikin gida, kamar motocin bas, da babura masu kafa biyu da kafa uku.

Alkaluma daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, fitar da motocin NEV na kasar Sin zuwa kasashen waje, ya karu da kashi 77.6 cikin dari zuwa sama da guda miliyan 1.2 a shekarar 2023. (Yahaya)