logo

HAUSA

Najeriya za ta fara samar da allurar zazzabin Lassa domin daina dogaro da na kasashen waje

2024-03-03 16:49:20 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta bayar naira biliyan 50 a matsayin kason farko ga asusun lura da lafiya na kasar, ninki a kan naira biliyan 25 da ta bayar a shekara ta 2022.

Ministan lafiya na kasar Farfesa Muhammed Ali Pate ne ya tabbatar da hakan a Abuja yayin taron manema labarai da ma’aikatar yada labarai ta saba shiryawa ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Ministan ya ce, samun karin wannan kudi, alama ce dake nuna kokarin gwamnati wajen tabbatar da ganin ta kawo sauyi mai ma’ana ta fuskar kiwon lafiyar al’ummar kasar, ta hanyar wadata asibitoci da kayan aiki da ma’aikata da kuma magunguna.

A game kuma da kokarin da gwamati take yi kuwa wajen tabbatar da ganin ta karfafa kamfanonin samar da magunguna a cikin gida da kuma baiwa na kasashen waje damar saka jarinsu a bangaren samar da masana’antun samar da magunguna a Najeriya, ministan lafiyar ya ce, tuni hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar da kuma hukumar tabbatar da ingancin abinci da maguguna na kasar, tare da hadin gwiwa da abokan hulda na kasashen ketare suka fara nazari a kan cutar Lassa da nufin samar da allurar cutar a Najeriya ta yadda za ta wadata sosai.

A game da sauran magunguna ma, ministan ya bayyana cewa, “Yanzu haka akwai a kalla kamfanoni uku da za su shigo Najeriya, inda tuni wani kamfani daga kasar Brazil ya fara nuna yunkurinsa wajen amincewa da kashe dola miliyan 240 a matsayin jari da zai saka a bangaren masana’antun samar da magunguna na Najeriya.” (Garba Abdullahi Bagwai)