logo

HAUSA

An bude taron kasashe masu arzikin iskar gas karo na 7 a Algiers

2024-03-03 17:26:56 CMG Hausa

A jiya Asabar ne aka bude taron koli karo na 7 na dandalin kasashe masu arzikin iskar gas ko GECF a takaice, da nufin kare muradun masu samar da iskar gas da masu amfani da shi.

A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Algeriya Abdelmadjid Tebboune ya jaddada muhimmiyar rawar da dandalin ke takawa wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta a wannan zamani, da samar da ci gaba mai dorewa, da kuma biyan bukatar makamashi a duniya.

Manyan jami'ai da shugabannin masana'antu daga Qatar, Iraki, Mauritania, Tunisiya, Iran, Senegal, Mozambique, Bolivia, da Libya sun halarci taron, wanda ya yi nuni da wakilcin kasashe daban-daban da suka kuduri aniyar tsara makomar makamashin duniya.

GECF mai hedikwata a Doha, yana da mambobi 12 na dindindin da suka hada da Algeriya, Bolivia, Masar, Equatorial Guinea, Iran, Libya, Nijeriya, Qatar, Rasha, Trinidad and Tobago, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Venezuela, da ma mambobi bakwai masu sa ido. (Yahaya)