logo

HAUSA

IMF: Tattalin arzikin kasar Sin ya farfado a shekarar 2023

2024-03-03 17:22:53 CMG Hausa

Sassan tattalin arzikin kasar Sin sun sake farfadowa a shekarar 2023 biyo bayan sake bude kasar bayan COVID-19 yayin da ainihin GDPn da aka yi kiyasi ya karu sosai daidai da manufar ci gaba da mahukuntan kasar suka tsara ta kusan kashi 5 cikin dari, a cewar kwamitin zartarwa na asusun ba da lamuni na duniya IMF.

Asusun na IMF ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na baya bayan nan bayan kammala nazari na shekara kan bayani na hudu na tattalin arzikin kasar Sin.

A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon IMF, bukatun cikin gida musamman sayayyar ‘yan kasar ne ya haifar da murmurewar, da kuma taimakon manufofin inganta sassan tattalin arzikin, da suka hada da karin sassauta manufofin kudi, rage haraji ga kamfanoni da gidaje, da kashe kudi don ba da agaji ga bala'o’i.  .

Tawagar IMF ta ziyarci kasar Sin daga ranar 26 ga watan Oktoba zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba, domin gudanar da shawarwarin da aka yi a kan bayanin na IV na shekarar 2023.

Tawagar ta yi tattaunawa mai ma'ana tare da manyan jami'an gwamnati da na babban bankin kasar Sin, da wakilan kamfanoni masu zaman kansu da masana ilimi, inda suka yi musayar ra'ayi kan makomar tattalin arzikin kasar Sin da hadarin da ka iya faruwa a gaba, da manufofin da za a dauka da sauransu. (Yahaya)