logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Jigawa za ta ci gaba da aikin titunan mota 17 dake sassan jihar

2024-03-02 15:49:37 CGTN HAUSA

 

Majalissar zartarwar jihar Jigawa dake arewacin Najeriya ta amince da fitar da tsabar kudi har naira biliyan 13.5 domin kammala ayyukan ginin wasu tituna 17 a sassan jihar daban daban, tare kuma da sayo kayan abinci don rabawa kyauta ga masu karamin karfi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Sagir Musa ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan da kammala taron majalissar, inda ya ce, ana son a gaggauta kammala ayyukan kafin faduwar damunar bana.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.