logo

HAUSA

Sashen kera batiran lithium na kasar Sin ya bunkasa da kaso 25 bisa dari a bara

2024-03-02 16:18:34 CMG Hausa

Wasu alkaluma na ma'aikatar raya masana'antu da fasahar sadarwar kasar Sin, sun nuna yadda sashen kera batiran lithium na kasar ya samu ci gaba da kaso 25 bisa dari a shekarar 2023 da ta gabata.

Alkaluman sun nuna yadda jimillar karfin batiran da aka sarrafa a kasar a baran, ya kai sa'o'in gigawatt 940. Adadin da darajarsa ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.4, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 197. (Saminu Alhassan)