logo

HAUSA

Sin ce ta daya a duniya a yawan adadin tace mai a shekarar 2023

2024-03-02 16:13:14 CMG Hausa

Wani rahoto da cibiyar bincike karkashin kamfanin man fetir na kasar Sin ta fitar, ya nuna cewa Sin din ce ta daya a duniya a yawan man fetir da kasashe ke tacewa, inda adadin man da kasar ta tace a shekarar 2023 ya daga zuwa tan miliyan 936.

Adadin man fetir da aka yi amfani da shi a kasar Sin a shekarar ta bara, ya kai kimanin tan miliyan 756, kana adadin man da aka sarrafa a shekarar ya kai tan miliyan 738, adadin da duka suka kai matsayin koli.

A daya bangaren, adadin tacaccen man fetir da aka yi amfani da shi a kasar ta Sin a shekarar ya kai tan miliyan 399, adadin da ya karu da kaso 9.5 bisa dari a shekara guda.

A shekarar ta 2023, adadin makamashi da Sin ta samar ya wadata, ya kuma daidaita. Kaza lika adadin danyen mai da Sin ta samar ya kai tan miliyan 200, adadin da ya ci gaba da karuwa shekaru 6 a jere. (Saminu Alhassan)