logo

HAUSA

Han Zheng ya yi kira ga sassan ‘yan kasuwar Sin da na Amurka da su bunkasa amincewa juna

2024-03-02 20:42:41 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya yi kira ga sassan ‘yan kasuwar Sin da na Amurka, da su bunkasa ginshikin abota, da amincewa da juna, da fadada sassan hadin gwiwa.

Han Zheng ya yi kiran ne a Juma’ar nan a birnin Beijing, yayin da yake jawabi ga mahalarta liyafar shekara shekara, ta yaba gudummawar cibiyar raya cinikayyar Amurka dake kasar Sin ko “AmCham China".(Saminu Alhassan)