logo

HAUSA

Firaministan Thailand: Cudanya da juna bisa shawarar ziri daya da hanya daya na raya ci gaban shiyyoyi

2024-03-02 15:38:39 CMG Hausa

A kwanakin baya ne firayin ministan kasar Thailand Srettha Thavisin, ya zanta da wakiliyar CMG, inda ya yi matukar jinjinawa shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar. A cewarsa, cudanya tsakanin kasa da kasa yana da muhimmanci kwarai, kuma cudanyar juna da ake yi yanzu, bisa shawarar gina ziri daya da hanya daya, tana ingiza ci gaban shiyyoyi yadda ya kamata.

Thavisin ya ce, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, Sin ce kasa mafi zuba jarin kai tsaye a Thailand, musamman ma a bangaren kera motocin dake amfani da wutar lantarki. A daya bangaren kuwa, Thailand ta fitar da manufar buga harajin gata, kuma ta samar da damammakin cin gajiyar juna, da gina tashoshin ruwa mai zurfi, da kuma yankunan masana’antu.

Firaministan na Thailand ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi ta Thailand ta samu ci gaba cikin sauri, har ta kai sahun gaba a shiyyar da take.

An lura cewa, kaso 40 bisa dari na motocin da aka yi oda yayin bikin baje kolin motocin da aka harhada a kasar a bara, motoci ne dake amfani da sabbin makamashi, kuma kaso 80 bisa dari na motocin na da tamburan kamfanonin kasar Sin.  (Jamila)