logo

HAUSA

Shugabannin Afirka sun yi kira da a karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban don magance matsalar muhalli

2024-03-01 10:48:38 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne a Nairobi, babban birnin kasar Kenya aka bude babban taro na shida na taron Majalisar Dinkin Duniya kan Muhalli (UNEA-6), inda shugabannin Afirka suka sabunta kira da aka yi na farfado da tsarin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, don habaka aiki a kan barazanar da duniya ke fuskanta, gami da sauyin yanayi, hasarar muhalli da gurbatar muhalli. 

Shugaban kasar Kenya William Ruto, a cikin jawabinsa ga majalisar ya ce, bisa la’akari da irin barazanar da duniya da mazaunanta ke fuskanta, akwai bukatar a samar da matsaya ta bangarori daban-daban, wadda za ta samar da mafita mai dorewa. 

Shugabannin kasashen Afirka da gwamnatocin sun halarci taron na yini biyu, wanda aka yi a karkashin taken "inganci, hada kai da dorewar matakai na bangarori daban-daban don tinkarar sauyin yanayi, hasarar rayayyun halittu da gurbatar muhalli."

Ruto ya kara da cewa, al'ummomin Afirka marasa galihu na fuskantar barazana, sai dai idan an yi kokarin shawo kan matsalolin sauyin yanayi, gurbatar ruwa, da yin amfani da nau'o'in halittu fiye da kima da kuma lakumewar lemar sararin samaniyar. (Muhammed Yahaya)