logo

HAUSA

Sin ta yi Allah wadai da kisan Falasdinawa fararen hula da sojojin Isra’ila suka yi

2024-03-01 19:18:37 CMG Hausa

A yau Juma’a ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ta yi matukar kaduwa da Allah wadai da harbin kan mai uwa da wabi, da sojojin Isra’ila suka yiwa Falasdinawa fararen hula a birnin Gaza. A hannu guda tana mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Mao Ning ta bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na rana rana da ta jagoranta, lokacin da aka yi mata tambaya game da harbin fararen hula Falasdinawa da sojojin Isra’ila suka yi a baya bayan nan.

Jami’ar ta ce Sin na fatan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, musamman tsagin Isra’ila, za su gaggauta dakatar da bude wuta, su tabbatar da kare lafiyar fararen hula, da bayar da damar shigar da kayan jin kai, tare da dakile kara tabarbarewar yanayin jin kai.

Game da matakin Amurka na hana kwamitin tsaron MDD fitar da sanarwa mai alaka da kisan Falasdinawa fararen hula dake kokarin karbar kayan tallafi a Gaza kuwa, Mao ta ce kamata ya yi manyan masu fada a ji, su rungumi manufar adalci da sanin ya kamata, su kuma taka rawar gani wajen ingiza matakin dakatar da bude wuta.

Da ta tabo batu game da damuwar da majalissar gudanarwar Amurka ta nuna don gane da digon 23 na kudurin doka na yankin Hong Kong kuwa, Mao Ning ta ce harkokin yankin Hong Kong batutuwa ne na cikin gidan Sin, don haka babu wata kasar waje dake da ikon tsoma baki, ko fusta kalamai marasa dalili kan su.

A fannin shirin gwamnatin Amurka na bincikar ababen hawa masu aiki da lantarki da ake kerawa a kasar Sin kuwa, Mao ta ce Sin na fatan Amurka za ta dakatar da yunkurin danne kamfanonin Sin, ta bude kofar samar da tsarin hada hadar kasuwanci a bude, bisa adalci, ba tare da nuna banbanci ba.  (Saminu Alhassan)