logo

HAUSA

Dalibai 20 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar Sankarau a jihar Yobe dake arewacin Najeriya

2024-03-01 09:45:09 CMG Hausa

A kalla dalibai 20 daga makarantun sakandire na kwana a jihar Yobe dake arewacin Najeriya ne aka bada labarin sun mutu saboda kamuwa da cutar sankarau.

Daliban kamar yadda rahotanni suka bayyana sun fito ne daga makarantu sakandaren kananan hukumomin Potiskum da Fika da kuma Fune.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Makarantun da aka sami rahoton mutuwa sakamakon wannan annoba sun hada da kwalejin kimiya da fasaha ta maza dake Potiskum da kuma kwalejin gwamnatin tarayya ta mata dake dai karamar hukumar ta Potiskum, inda daliba guda aka bada da labarin ta rasu, kamar yadda kwamishinan lura ilimin manya da kananan makarantu sakandare na jihar ta Yobe Dr. Muhammad Sani Idris ya tabbatar.

Ya ce yanzu haka gwamnati ta dauki matakai domin dakile yaduwar cutar zuwa wasu makarantun, kuma yanzu haka an killace daliban da suka kamu da wannan annoba a wata cibiya ta musamman a karamar hukumar Potiskum inda a nan ne cutar ta fi kamari.

“An samar da wanann cibiya ce hususan domin dakile yaduwar cutar, kuma a kalla dalibai 112 ne aka kwantar a wajen, kuma an samar da jami’an kiwon lafiya daga manya da kananan asibitoti. A yanzu haka dai akwai dalibai 43 da ake ci gaba da kula da su yayin da kuma aka salami 69.”

An dai alakanta bullar cutar a wadannan makarantu bisa cunkuso a dakunan kwanan dalibai da rashin wutar lantarki kana da matsalar yanayin abinci.

(Garba Abdullahi Bagwai)